Maganar Valdes zuwa Besiktas ta bi ruwa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Valdes ya ki ya buga wasa ne a cikin matasan United 'yan kasa da shekaru 21

An samu tsaiko kan batun komawar mai tsaron ragar Manchester United, Victor Valdes zuwa Besiktas ya taka leda.

Wata majiya dake kusa da Valdes ta ce Besiktas ce ta yi kokarin sauya wani sashi na yarjejeniyar da dan wasan ya amince da ita tun farko.

Valdes tsohon dan wasan Barcelona ya samu rashin jituwa tsakaninsa da kocin United Louis van Gaal shi ya sa ba a saka shi a wasanni.

Dan kwallon ya saka hannu a kan yarjejeniyar watanni 18 da United a watan Janairu, sai dai kuma Van Gaal ya soki dan wasan da kin buga tamaula a cikin matasa 'yan kasa da shekaru 21 na kungiyar.

A ranar Talata za a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasan tamaula a Ingila da Scotland, amma sai a ranar Litinin yawancin kasuwannin Turai za su rufe hada-hada.