Chelsea na daf da daukar Papy Djilobodji

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea tana mataki na 13 a kan teburin Premier da maki hudu

Chelsea na shirin sayo dan kwallon Senegal, Papy Djilobodji mai taka leda a Nantes kan kudi £4m.

Djilobodji mai tsaron baya zai ziyarci Stamford Bridge domin a duba koshin lafiyarsa, bayan da kungiyoyin biyu suka cimma yarjejeniya.

Kocin Chelsea Jose Mourinho na kokarin daukar Djilobodji, bayan da Everton ta ki sayar masa da mai tsaron bayanta John Stone.

Djilobodji wanda saura shekara daya kwantiraginsa ya kare a Nantes, ya buga mata wasanni 160 tun lokacin da ya koma can da taka leda a 2010.

Chelsea wacce ke rike da kofin Premier bara an ci ta kwallaye tara a wasanni hudu da ta buga a gasar Premier ba.