United ta koma cinikin De Gea da Real Madrid

Image caption Har yanzu United ba ta saka shi a wasannin Premier hudu da ta buga da kuma na kofin zakarun Turai biyu ba

Manchester United ta koma tattaunawa da Real Madrid kan sayar mata da mai tsaron ragarta David De Gea.

Tun da aka bude kasuwar saye da sayar da 'yan kwallon Turai ta bana, Real Madrid ta nuna sha'awar daukar De Gea din.

Sai a shekarar 2016 ne kwantiragin mai tsaron ragar De Gea zai kare da Manchester United.

United ta dage da cewa sai dai su yi musayar 'yan wasa, a inda ta bukaci bayar da De Gea sannan Real Madrid ta ba ta Sergio Ramos.

Tuni mai tsaron bayan Real Madrid Ramos ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da buga tamaula a Bernabeu.