Cinikin De Gea ya rushe

David de Gea Hakkin mallakar hoto All Sport
Image caption David de Gea

An samu tangarda a yunkurin da Manchester United ke yi na ganin mai tsaron ragarta David De Gea ya koma Real Madrid , saboda rashin gabatar da takardun cinikin a kan lokaci.

Manchester United ta amince ta sayar da De Gea a kan fam miliyan 29.

Sai dai kawo yanzu Manchester United da kuma Real Madrid ba su fitar da wata sanarwa ba a hukumance.

A karkashin yarjejeniyar United ta so Real Madrid ta ba ta dan wasanta Keylor Navas.

Ba a taba samun wani yanayi ba da aka karawa wata kungiya a Spaniya lokaci na saye ko sayar da yan wasan ba kamar yadda ake yi a Ingila.

Bangarorin sun fara zargin juna da haifar da jinkirin

Tun da aka bude kasuwar saye da sayar da 'yan kwallon Turai ta bana, Real Madrid ta nuna sha'awar daukar De Gea din.

Sai a shekarar 2016 ne kwantiragin mai tsaron ragar De Gea zai kare da Manchester United.

A yau ne wa'adin kasuwar saye da sayar da yan wasa na Turai ya zo karshe.