Modibo Maiga ya bar West Ham United

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Kwallaye bakwai Maiga ya ci wa West Ham a wasanni 45 da ya yi a kulob din

Dan kwallon West Ham, Modibo Maiga ya koma Al Nassr ta kasar Saudi Arabia da murza leda.

Maiga mai shekaru 27, dan kasar Mali ya saka hannu kan kwantiragin shekarun biyu da Al Nassr.

Dan wasan ya koma West Ham da murza leda kan kudi £4.7m daga Sochaux shekaru uku da suka wuce, amma ya koma buga wasannin tamaula aro a QPR da kuma Metz.

Maiga wanda ya shiga wasa daga baya, shi ne ya ci kwallo ta uku da suka doke Bournemouth 4-3 a makwon jiya a gasar Premier.