Wolfsburg ta dauko Dante da Draxler

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Drexler ya bar Schalke domin ya buga wa Worlfsburg tamaula

Wolfsburg ta kammala sayo Julian Draxler da kuma dan kwallon Bayern Munich Dante.

Dante dan kwallon Brazil ya saka hannu kan yarjejeniyar shekaru uku, yayin da Draxler dan wasan Schalke ya amince da kwantiragin shekaru biyar.

Sai dai kuma Wolfsburg ba ta bayyana jumullar kudin da ta dauko 'yan wasan biyu ba.

Wolsburg wacce ta sayar da Kevin De Bruyne ga Manchester City kan kudi £55m a ranar Lahadi ce ta sanar da sayen 'yan wasan biyu ranar Litinin.

Haka kuma kungiyar wacce ke buga Bundesliga tana rukuni da ya hada da Manchester United a gasar cin kofin zakarun Turai.