Chelsea ta dauki Papy Djilobodji daga Nantes

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea tana mataki na 13 a kan teburin Premier da maki hudu

Chelsea ta sayo dan kwallon Senegal, Papy Djilobodji mai taka leda a Nantes kan kudi £4m.

Djilobodji mai tsaron baya, mai shekaru 26, ya saka hannu a Stamford Bridge kan yarjejeniyar shekaru hudu.

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya dauki Djilobodji ne bayan da Everton ta ki sayar masa da mai tsaron bayanta John Stone.

Djilobodji wanda saura shekara daya kwantiraginsa ya kare a Nantes, ya buga mata wasanni 160 tun lokacin da ya koma can da taka leda a 2010.

Chelsea wacce ke rike da kofin Premier bara an ci ta kwallaye tara a wasanni hudu da ta buga a gasar Premier ba.