Man United ta sayi Martial kan kudi £36m

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya ci kwallaye takwas a Monaco a bara

Manchester United ta sayi dan kwallon Monaco, Anthony Martial kan kudi £36m.

Monaco ta bai wa Martial mai shekaru 19, wanda Arsenal ta dade tana zawarci izini a ranar Litinin da ya je Old Trafford domin a duba koshin lafiyarsa.

Dan wasan ya ci kwallaye takwas daga wasanni 31 da ya yi a gasar Faransa wato Ligue 1 a bara.

Martial ya zama dan wasa na uku da United ta dauka mafi tsada a tarihi, bayan Angel Di Maria da ta biya £59.7m daga Real Madrid da kuma Juan Mata da ta dauko daga Chelsea kan kudi £37.1m.

Dan wasan ya fara murza leda a Lyon a matsayin kwararren dan wasa a watan Disambar 2012, daga nan ya koma Monaco da taka leda a watan Yunin 2013.