Ranar karshe ta musayar 'yan kwallo

Yayin da wa'adin kasuwar saye da sayar da 'yan wasan kwallon kafa ke karewa a ranar Talata, rahotanni na nuna cewa I zuwa yanzu kudin da kungiyoyin kwallon kafa na Ingila suka kashe bai kai na bara ba.

Kudaden da kungiyoyin suka kashe a makon da ya gabata sun kai kimanin Pam miliyan 680, wanda a bara kuwa an kashe Pam miliyan 835.

Kazalika, adadin na shekarar 2015 ya dara na bara a daidai wannan lokaci da kaso hudu cikin 100.

Rahotanni na nun cewa kafin wa'adin ya gama karewa a ranar Talata, ga alama kungiyoyin kwallon kafa za su kafa sabon tarihi na kashe kudi.

"Yaushe ne lokacin rufe cinikin?"

Image caption Ko za a iya sayen wadannan 'yan wasan kafin wa'adin saye da sayarwan ya cika?

A Ingila, za a rufe cinikin saye da sayar da 'yan wasa na gasar Firimiya da na gasar kwallon kafa da misalin karfe shida agogon kasar ranar Talata daya ga watan Satumba.

Sa'o'i shida bayan nan kuma da tsakar dare za a rufe saye da sayar da 'yan wasa a Scotland.

An kara wa'adin ne daga ranar 31 ga watan Agusta saboda dokar Firimiya ta hana kawo karshen wa'adin a ranar hutu na kasa.

Kungiyar gasar Firimiya ta yanke shawarar sanya karfe shida na yamma ya zamo cikar wa'adin ne saboda wa'adin mika tawagar sunayen 'yan wasa ga kungiyar gasar zakarun Turai zai kawo karshe da misalin karfe 11 na dare.

Mafi akasarin kungiyoyin kwallon kafa na Turai kamar su Jamani da Faransa da Sipaniya da kuma Netherlands sun rufe cinikin 'yan wasa ne a ranar Litinin 31 ga watan Agusta.

Karewar wa'adin zai shafi sayen 'yan wasa ne kawai, wanda hakan ke nufin kungiyoyin kwallo na Ingila za su iya sayen 'yan wasa daga kungiyoyin wasu kasashen har sai an rufe cinikin a Ingila.

"Wadanne ne manyan musayar da aka yi zuwa yanzu"

Babban cinikin da aka yi shi ne na komawar Kevin de Bruyne kungiyar Manchester City daga Wolfsburg inda aka biya Pam miliyan 55, wanda ya disashe cinikin da aka yi na Pam miliyan 44 lokacin da ta dauko Raheem Sterling daga Liverpool.

Wadannan musaya suna cikin guda bakwai wadanda Manchester City ta yi da bazarar nan, wadanda suka hada da sayen Fabian Delph da Patrick Roberts da kuma Nicolas Otamendi.

Kazalika kungiyar Manchester United ma ta kashe kimanin Pam miliyan 83 domin sayen Memphis Depay da Matteo Darmian da Bastian Schweinsteiger da kuma Morgan Schneiderlin.

Chealse kuwa ta ja kafa ne lokacin da aka bude kasuwar sayen 'yan kwallon inda aka bar ta da sayen 'yan wasa biyu kacal Pedro da Baba Rahman.

"Wadanne manyan musaya za a iya yi kafin wa'adin ya cika?"

Chelsea za ta iya ci gaba da sayen 'yan wasa a kurarren lokaci inda za ta sanya hannu wajen sayan mai tsaron baya na Everton John Stones.

Wani dan wasan kuma da ake cinikinsa don ya bar kungiyarsa ta West Brom shi ne Saido Berahino, wanda Tottenham ta taya shi sau biyu kan kudi Pam miliyan 18 da kuma Pam miliyan 22.