West Brom ta sayi Joleon Lescott

Hakkin mallakar hoto rex features
Image caption Lescott tsohon dan kwallon Manchester City

Mai tsaron bayan kungiyar Aston Villa, Joleon Lescott ya koma West Brom da taka leda kan kudin da ake cewa zai kai £2m.

Lescott mai shekaru 33, dan kwallon Ingila ya buga wa Wolves da Everton da kuma Manchester City tamaula.

Sai dai kuma Aston Villa ta dauki Matija Sarkic daga Anderlecht kan yarjejeniyar shekaru uku.

Haka kumma Villa din ta ce ba za ta dauki Berbatov dan kwallon Monaco wanda kwantiraginsa ya kare a bana da kulob din Faransa.