Za a yi wasannin Commonwealth a Durban

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Karo na farko da za a yi wasannin Commonwealth a nahiyar Afirka

Durban zai kasance birni na farko a Afirka da zai karbi bakuncin wasannin Commonwealth, bayan da aka amince ya karbi wasannin da za a yi a 2022.

Durban da ke Afirka ta Kudu ne ya rage a cikin 'yan takara, bayan da birnin Edmonton ya janye daga neman wasannin a watan Fabarairu bisa matsalar karancin kudi.

Za a fara wasannin ne a ranar 18 ga watan Yuli, kuma karo na 22 kenan da za a gudanar da wasannin da ake yi a duk shekaru hudu.

Dukkan kayayyakin da ake bukata domin gudanar da wasannin an tanade su a Durban din, in banda shinfida filin wasan guje-guje da ya rage.

Durban din ya ci gajiyar katafaren filin wasa na Moses Mabhida wanda ya karbi bakuncin gasar cin kofin duniya da aka yi Afirka ta Kudu a 2010.