Ni na ki komawa Milan karo na biyu - Ibrahimovic

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ibrahimovic ya ce zai ci gaba da yin wasanninsa a PSG

Dan wasan Paris St-Germain, Zlatan Ibrahimovic ya ce shi ne ya ki amincewa da ya koma AC Milan karo na biyu da taka leda a lokacin cinikayyar 'yan wasan tamaula ta Turai.

Ibrahimovic mai shekaru 33, ya lashe kofin gasar Holland a Ajax da Intermilan da Barcelona da PSG da kuma wanda ya dauka da Milan a 2011.

An yi ta rade-radin cewar dan wasan zai koma Arsenal ko Fenerbahce ko kuma Galatasaray da murza leda kafin a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasan kwallon kafa.

Ibrahimovic ya kara de cewar a baya ya fada cewar zai ci gaba da wasa a PSG, domin hankalinsa a kwance yake a kulob din.

Ya kuma ce AC Milan sun yi masa tayin ya sake komawa can karo na biyu da murza leda, kuma ya ji dadi domin hakan ya nuna yana yin kwazo a tamaula kena.