Tom Cleverley na Everton zai yi jinya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Cleverly zai yi jinya mai tsawo kafin ya dawo fagen murza leda

Dan kwallon Everton, Tom Cleverly zai yi jinya mai tsawo bisa raunin da ya ji a kafarsa, koda yake da farko an dauka ya gamu da karaya ne.

Sai sauya Cleverly mai shekaru 26, aka yi bisa karo da ya yi da Eric Dier a karawar da suka yi da Tottenham a gasar Premier ranar Asabar.

Kocin Everton Roberto Martinez ya ce raunin da Clerverly ya ji ya zo da sauki, domin sun za ta ya samu karaya ne.

Cleverley ya koma Everton da taka leda daga Manchester United ranar 1 ga watan Yuli, bayan da ya gama buga wasa aro a Aston Villa.