West Brom za ta gana da Saido Berahino

Image caption Berahino ya ce ba zai sake buga wasa a West Brom karkashin Jeremy Peace

West Brom za ta tattauna da Saido Berahino, bayan da Tottenham ta kasa daukar dan kwallon a ranar karshe da za a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallon Turai.

West Brom za ta ci tarar Berahino mai shekaru 22, a kan furucin da ya yi a shafinsa na twitter a inda ya soki Jeremy Peace shugaban kungiyar.

Peace ya ki sallama tayi biyu da Tottenham ta yi wa Berahino, a inda shugaban ya ce Spurs ta yi kokarin daukar dan wasan ne a arha.

West Brom za ta tattauna da Berahino da kocin kungiyar Tony Pulis da kuma wasu jami'an kungiyar.

West Brom ta ce tayin da Tottenham ta yi wa Berahino ya yi kadan bai kai darajar da suka yi masa ba.