Enyeama ba zai buga wa Najeriya wasa ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Enyeama ba zai buga wasan ba saboda rashin mahaifiyarsa

Golan Najeriya, Vincent Enyeama ya fita daga jerin 'yan wasan da za su taka leda a wasan da Najeriya za ta kara da Tanzania domin neman cancantar buga wasan kofin Afirka na shekara ta 2017. Ya janye jikin ne dai sakamakon rasuwar mahaifiyarsa.

Tun da farko dai, kamata ya yi a ce Enyeama wanda ya buga wa kulob din Lille na Faransa wasa ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja amma kwatsam sai ya soke tafiyar tasa.

Dan wasan dai ya wallafa a shafinsa na Instagram ranar Laraba yana mai neman afuwar 'yan kasar bisa rashin fafatawarsa a wasan da Najeriya za ta buga da Tanzania. Sai dai kuma bai fadi dalili ba.

Amma daga baya bayanai sun nuna cewa rashin halartar tasa tana da alaka da rashin mahaifiyarsa.

Wannan bayanin dai ya fito ne 'yan sa'o'i kadan bayan da kocin Super Eagles, Sunday Oliseh ya sanar da kafafen yada labarai cewa Enyeama ya fita daga jerin 'yan wasan da za su kara da kungiyar wasa ta Taifa Stars da ke Tanzania.

Yanzu haka gola Carl Ikeme ne zai maye gurbin Enyeama din.