'Ina takaicin masu karyar jin rauni'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jack Butland yana bakin cikin masu karya da rauni

Golan Ingila, Jack Butland ya ce abun da ke kona masa rai shi ne idan ya ga 'yan uwansa 'yan kwallo suna karyar samun rauni a filin wasa.

Ya ce "Ko yaushe abin yana ba ni takaici. Abu ne da na tsana. Ina son na je na daga mutane".

Butland dai ya karya yatsa a lokacin wasan atasaye makonni biyu da suka wuce.

Kuma an yi tsammanin cewa dan wasan mai shekaru 22, ba zai buga wasanni ba har na tsawon makonni shida sakamakon raunin da ya ji.

To amma sai ga shi ya bayyana a wasannin da kulob din ya buga da Norwich a inda aka tashi daya da daya.