Manchester United ba ta 'goge' ba - Perez

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption De Gea ya nuna sha'awar komawa Real

Shugaban kungiyar Real Madrid ya ce Manchester United ba ta da "gogewa" a kasuwar musayar 'yan kwallo, shi ya sa David De Gea bai koma Real Madrid ba.

Florentino Perez ya ce lamarin ya yi daidai abin da ya faru a Fabio Coentrao da kuma Ander Herrera a shekara ta 2013.

Perez ya ce "Basu goge ba."

"Haka abin ya kasance da Coentrao da kuma Herrera."

Real Madrid da Manchester United sun zargi juna a kan batun kasa kulla cinikin De Gea.

Kungiyar ta Spain ta ce ta yi iyaka kokarinta domin sayen golan mai shekaru 24 amma sai aka samu kuskure cikin minti biyu.