Euro 2016: Ingila ta kai gasar cin kofin nahiyar Turai

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rooney na fatan karya tarihin dan wasa da ya fi cin kwallaye a Ingila

Ingila ta doke San Marino da ci 6-0 a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da suka fafata a ranar Asabar.

Wayne Rooney ne ya fara cin kwallo a bugun penariti a minti na 13 da fara tamaula, sauran 'yan wasan da suka ci kwallayen sun hada da Brolli da ya ci gida sai Barkley da Walcott da kuma Kane.

Kwallon da Rooney ya ci ya sa ya yi kan-kan-kan da Sir Bobby Charlton a matsayin 'yan wasan da suka fi yawan ci wa Ingila kwallaye, yayin da kowannensu ya zura 49 a raga.

Da wannan sakamakon Ingila ta yi wasa bakwai ta kuma lashe su gabaki daya, a inda ta hada maki 21 a rukuni na biyar ta kuma samu tikin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da Faransa za ta karbi bakunci a 2016.