Kai Tsaye: Bayanai kan wasanni

Latsa nan domin sabunta shafin

Barkanmu da ziyarta shafin BBC Hausa kai tsaye a kan wasanni. Za mu kawo muku labarai kan wasanni da ke faruwa a ranar Asabar musamman irin wainar da ake toyawa a nahiyar Turai dama duniya.

08:33 Wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka Lahadi 06 Satumba

 • 12:00 Mauritius vs Mozambique
 • 12:30 Madagascar vs Angola
 • 01:00 Lesotho vs Algeria
 • 01:00 Zimbabwe vs Guinea
 • 01:00 Kenya vs Zambia
 • 01:00 Swaziland vs Malawi
 • 03:00 Central African Republic vs Congo DR
 • 03:30 Chad vs Egypt
 • 04:00 Sierra Leone vs Ivory Coast
 • 04:00 Benin vs Mali
 • 05:30 Gambia vs Cameroon
 • 06:00 Libya vs Cape Verde

08:27 Wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai Lahadi 06 Satumba.

 • 05:00 Malta vs Azerbaijan
 • 05:00 Turkey vs Netherlands Atatürk Olympic Stadium
 • 05:00 Latvia vs Czech Republic
 • 05:00 Wales vs Israel
 • 05:00 Norway vs Croatia
 • 07:45 Italy vs Bulgaria
 • 07:45 Iceland vs Kazakstan
 • 18:45 Bosnia And Herzegovina vs Andorra
 • 07:45 Cyprus vs Belgium

07:52 Sudan ta Kudu ta lashe wasan farko tun zama mamba a fifa a 2012, a inda ta doke Equatorial Guinea da ci 1-0.

Atak Lual ne ya ci kwallon a minti na 52 a karawar tarihi da suka yi a Juba, kuma da wannan sakamakon Sudan ta Kudun tana mataki na biyu a rukuni na uku, yayin da Benin da Mali za su kara a ranar Lahadi.

07:43 Wasu sakamakon wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai

 • Luxembourg 1 - 0 Macedonia
 • Ukraine 3 - 1 Belarus
 • Estonia 1 - 0 Lithuania
 • San Marino 0 - 6 England
 • Russia 1 - 0 Sweden

07:38 Wayne Rooney ya yi kan-kan-kan da Sir Bobby Charlton a matsayin wadanda suka fi ciwa Ingila kwallaye a raga, a inda kowannensu ya ci 49. Roney wanda kafin Ingila ta kara da San Marino ya zura kwallaye 48 ne a raga, kuma ya kara daya a ranar Asabar.

Hakkin mallakar hoto Reuters

05:16 Tanzaniya da Nigeria sun tashi wasa babu ci a karawar da suka yi a neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka a Dar es Salaam. http://bbc.in/1JHtx63

04:43 Za a take wasa da karfe 5:00 agogon Nigeria da Niger a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai.

 • Russia vs Sweden
 • Estonia vs Lithuania
 • Ukraine vs Belarus
 • Luxembourg vs Macedonia
 • San Marino vs England

04:33 Wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a buga Asabar 05 Satumba

 • Sao Tome And Principe vs Morocco
 • Guinea-Bissau vs Congo
 • Liberia vs Tunisia
 • Gabon vs Sudan
 • Mauritania vs South Africa

04:30 Sakamakon wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka

 • Comoros 0 : 1 Uganda
 • Seychelles 1 : 1 Ethiopia
 • Burundi 2 : 0 Niger
 • Tanzania 0 : 0 Nigeria
 • Rwanda 0 : 1 Ghana
 • Namibia 0 : 2 Senegal
 • South Sudan 1 : 0 Equatorial Guinea

03:54 Faransa ta doke Portugal da ci daya mai ban haushi a wasan sada zumunta da suka buga ranar Juma a.

Farance ta zura kwallo ne ta hannun Mathieu Valbuena wanda ke taka leda a Lyon. Faransa din za ta kuma kara da Serbia a wani wasan sada zumuntar a Bordeaux da yammcin Litinin.

Hakkin mallakar hoto AFP

03:37 Tanzania 0 vs Nigeria 0

'Yan wasan da suke buga wa Nigeria wasan: Carl Ikeme; SOLOMON KWAMBE, Kingsley Madu, William-Troost Ekong, Kenneth Omeruo, Nwankwo Obiora, Haruna Lukman, Moses Simon, Ahmed Musa, Izunna Uzochukwu, Emmanuel Emenike

Masu jiran karta kwana: Ikechuku Ezenwa; Chima Akas, Godfrey Oboabona, Rabiu Ibrahim, Emem Eduok, Sylvester Igboun, Anthony Ujah

03:30 An je hutun rabin lokaci a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin Africa.

 • Seychelles 1 : 0 Ethiopia
 • Tanzania 0 : 0 Nigeria
 • Rwanda 0 : 0 Ghana
 • Namibia 0 : 1 Senegal
 • Burundi 1 : 0 Niger
 • South Sudan 0 : 0 Equatorial Guinea

03:07 Labaran da wasu jaridun Turai suka wallafa da suka shafi cinikin 'yan wasan tamaula kafin a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallon.

Gazzetta Dello Sport: Paul Pogba ya ki amince wa da tayin £62m da Chelsea ta yi masa duk da Juventus ta amince ya koma Stamford Bridge da murza leda a lokacin da ake tsaka da hada-hadar saye da sayar da 'yan wasan kwallon kafa na Turai.

Sun: Shugaban Bayern Munich Karl-Heinz Rummenigge ya ce sun ki yin na'am da tayi mai tsoka da Manchester United ta yi wa Thomas Muller kafin a rufe kasuwar cinikayyar 'yan wasan Tamaula ta Turai.

Daily Mail: Mai tsaron ragar Tottenham, Hugo Lloris ya ce saura kiris ya koma Manchester United da wasa a lokacin da ake saye da sayar da 'yan wasan Turai.

02:45 Wannan dambe ne da aka taka na turmi daya tsakanin Sarki Ashiru Horo daga Arewa da Sarki Shagon Mada daga Kudu da suka yi a Abuja. Babu kisa a wannan wasan.

02:37 Sakamakon wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da aka yi a ranar Juma a 04 ga watan Satumba.

 • Georgia 1 - 0 Scotland
 • Germany 3 - 1 Poland
 • Gibraltar 0 - 4 R. of Ireland
 • Faroe Islands 1 - 3 Northern Ireland
 • Greece 0 - 1 Finland
 • Hungary 0 - 0 Romania
 • Denmark 0 - 0 Albania
 • Serbia 2 - 0 Armenia

02:34 Wasu daga ra'ayoyin da kuke tafka muhawara a BBC Hausa Facebook

Boyes Saudiya: Tabbas Manchester United za mu taka rawar gani a kan wasan bana, duba da yadda muka yi sayayya masu amfani, up United for life.

Sabo Banga Lallai: Za mu kara fahintar komai kenan a fagen wasanni up arsenal up Real Madrid

02:26 Lee Selby zai kare kambunsa na IBF ajin featherweight a karon farko a damben boxing, zai kuma dambata ne da dan kasar Mexico Fernando Montiel a cikin watan Oktoba a Amurka.

A watan Mayu ne Selby ya lashe kambun IBF bayan da ya doke Evgeny Gradovich. Zai kuma kare kambunsa ne da zai fafata da Montiel ranar 14 ga watan Oktoba Gila River Arena in Phoenix, Arizona.

Hakkin mallakar hoto Getty

02:05 An fitar da Rafael Nadal daga gasar US Open a wasan zagaye na uku a ranar Juma a. Fabio Fognini ne dan kasar Italiya ya yi waje da shi da ci 3-6 4-6 6-4 6-3 6-4.

Wannan ne karon farko da zakaran US Open karo biyu Nadal aka doke shi a wasa, yayin da ya cinye karawa biyu a jere a wasa daga nan kuma ya yi rashin nasara a wasanni uku kai tsaye a karawa biyar da suka yi.

Da wannan sakamakon Fognini zai fafata da Feliciano Lopez na Spaniya a wasan zagaye na hudu na gasar.

Hakkin mallakar hoto AFP

01:38 Jamus ta dare mataki na daya a rukuni na hudu a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin Turai, bayan da a ranar Jumu a ta doke Poland da ci 3-1.

Thomas Muller ne ya fara cin kwallo sai Mario Gotze da ya ci biyu a karawar. Robert Lewandowski ya ci wa Poland kwallo.

Jamus ta yi wasanni bakwai tana da maki 16, sai Poland a matsayiu na biyu da maki 14.

Hakkin mallakar hoto Getty

01:20 Karawar da Ingila za ta yi da San Marino a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin Turai, Wayne Rooney na fatan doke tarihin yawan ci wa Ingila kwallaye a raga da Bobby Charlton ya zuwa 49 a tarihi. Rooney wanda ya fara buga wa babbar tawagar Ingila wasa a 2003, ya yi mata karawa sau England 105 ya kuma zura kwallaye 48 a raga.

Hakkin mallakar hoto Getty

12:57 Gasar Brasileirão wasannin makwo na 23. Sao Paulo vs Internacional Vasco da Gama vs Atletico MG

12:30 Wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin Nahiyar Turai

Hakkin mallakar hoto Reuters
 • 05:00 Ukraine vs Belarus
 • 05:00 Estonia vs Lithuania
 • 05:00 Luxembourg vs Macedonia
 • 05:00 Russia vs Sweden
 • 05:00 San Marino vs England
 • 07:45 Montenegro vs Liechtenstein
 • 07:45 Austria vs Moldova
 • 07:45 Switzerland vs Slovenia
 • 07:45 Spain vs Slovakia

12:26 Wasannin neman gurbin shiga gasar kofin Afirca, lokutan karawar dai-dai da agogon Nigeria da Niger.

Hakkin mallakar hoto AFP
 • 01:00 Comoros vs Uganda
 • 01:30 Seychelles vs Ethiopia
 • 02:30 Burundi vs Niger
 • 02:30 Namibia vs Senegal
 • 02:30 Rwanda vs Ghana
 • 02:30 Tanzania vs Nigeria
 • 03:00 Botswana vs Burkina Faso
 • 04:30 Sao Tome And Principe vs Morocco
 • 16:00 Liberia vs- Tunisia
 • 05:00 Guinea-Bissau vs Congo
 • 05:30 South Sudan vs Equatorial Guinea
 • 06:00 Mauritania vs South Africa
 • 06:00 Gabon vs Sudan