Tanzani da Nigeria sun tashi wasa 0-0

Image caption Wasan farko da Sunday Oliseh ya jagoranci Super Eagles

Tanzaniya da Nigeria sun tashi wasa babu ci a karawar da suka yi a neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka a Dar es Salaam.

Wannan kuma shi ne babbar karawa da sabon kocin Super Eagles Sunday Oliseh ya jagoranci Nigeria tun lokacin da ya maye gurbin Stephen Keshi.

Da wannan sakamakon Nigeria ta yi wasanni biyu tana da maki hudu a rukuni na bakwai, za kuma ta karbi bakunci Masar a ranar 23 ga watan Maris din 2016.

Nigeria ta doke Chad da ci 2-0 a wasan farko da ta yi a neman gurbin shiga gasar cin kofin Afirka a ranar 13 ga watan Yuni.

Ga sauran sakamakon wasu wasannin da aka buga:

  • Comoros 0 : 1 Uganda
  • Seychelles 1 : 1 Ethiopia
  • Burundi 2 : 0 Niger
  • Tanzania 0 : 0 Nigeria
  • Rwanda 0 : 1 Ghana
  • Namibia 0 : 2 Senegal
  • South Sudan 1 : 0 Equatorial Guinea