Drogba ya ci wa Montreal kwallaye 3 rigis

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasa na biyu kenan da Drogba ya buga wa Montreal tamaula

Didier Drogba ya zura kwallaye uku a wasa na biyu da ya buga wa Montreal tamaula a gasar Amurka da suka doke Chicago Fire da ci 4-3 a ranar Asabar.

Drogba mai shekaru 37, ya fara buga wa Montreal wasa a makwon jiya, a inda ya shiga fili a matsayin wanda ya canji dan wasa.

A ranar Asabar ne Montreal ta fara tamaula da shi a cikin fili da kuma hakan ya ba shi damar cin kwallaye uku da ya ba su damar samun maki uku a kan Chigo Fire da shi.

Drogba wanda ya koma Montreal daga Chelsea a watan Yuli, shi ne dan wasan da ya fi yawan ci wa Ivory Coast kwallaye a raga a inda ya ci 65 a wasanni 105 da ya yi mata.