Berahino zai dawo buga wasa - Gordon Taylor

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Berahino na fatan ya gwada sa a da wata kungiyar a bana

Shugaban kungiyar 'yan wasan tamaula Gordon Taylor ya ce Saido Berahino zai ci gaba da buga wa West Brom tamaula.

Berahino ya fada a baya cewar ba zai sake yi wa West Brom wasa ba karkashin shugaban kulob din Jeremy Peace, wanda ya hana cinikinsa zuwa Tottenham.

West Brom ta bai wa dan wasan dan Ingila mai shekaru 22 hutu, kuma zai gana da mahukuntan kungiyar a ranar Litinin.

Taylor ya sanar da BBC cewar sun tuntubi Berahino da kuma West Brom kan takaddamar dake tsakaninsu, kuma suna sa ran za a gano bakin zaren lokaci kankane.

Sau hudu Tottenham tana taya Berahino a inda West Brom ta ki sallama dan kwallon, sannan ba ta saka shi a wasanni uku da ta yi a baya ba.