Sakamakon wasannin damben gargajiya

Image caption Shagon Yahaya daga Arewa da Matawallen Kwarkwada daga Kudu, babu kisa a wannan takawar

A ci gaba da wasan damben gargajiya da aka yi ranar Lahadi a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja Nigeria, an kara a wasanni da dama.

An fara sa zare tsakanin Autan Faya daga Kudu da Bahagon Abba Na Bacirawa daga Arewa kuma turmi uku suka yi babu kisa.

Damben Shagon Dakaki daga Kudu da Shagon Bahagon Musa daga Arewa turmi biyu suka yi babu kisa aka raba wasan.

Shi ma wasa tsakanin Shagon Shagon Alhazai daga Arewa da Matawallen Kwarkwada daga Kudu turmi uku suka yi babu kisa Sarkin gida na Jafaru Kura ya raba fafatawar.

An kuma karkare da wasan Bahagon Sisco daga Kudu da Abban Na Bacirawa daga Arewa, kuma turmi uku suka kara babu kisa aka raba wasan aka kuma tashi daga filin wasa.