Ideye na fatan taka rawar gani a Girka

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ideye baya cikin 'yan wasan Nigeria da suka buga gasar kofin duniya a Brazil a 2014

Brown Ideye na fatan dawo da tagomashinsa a Olympiokos domin ya samu damar sake buga gasar cin kofin zakarun Turai.

Ideye bai taka rawar gani ba a Ingila, duk da sayen shi £10 da West Brom ta yi a matsayin dan kwallon da ta dauka mafi tsada a tarihi.

Ya buga wa West Brom wasanni 31 a inda ya ci kwallaye bakwai kacal.

Dan wasan ya Shaida wa BBC cewar "Ya ji dadi da ya dawo Girka da taka leda, zai kuma maida hankali domin ya dinga buga wasa akai-akai"

Ideye ya fara buga wa tawagar kwallon kafar Nigeria tamaula a watan Agustan 2010, ya kuma zura kwallaye biyar daga wasanni 24 da ya yi wa Super Eagles.

Dan kwallon yana daga cikin 'yan wasan da suka wakilci Nigeria a gasar cin kofin duniya da aka yi a Afirka ta Kudu.