Bolt ba zai yi tsere a Diamond League ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bolt na fatan kare kambunsa a gasar Olympic da za a yi a Brazil a 2016

Usain Bolt ba zai fafata a wasannin tsalle-tsalle da guje-guje da za a yi a Brussels ranar Juma'a ba, saboda hutun da zai yi na kakar wasannin bana.

Bolt mai shekaru 29, ya lashe tseren mita 100 da 200 da kuma na 400 na 'yan wasa hudu da aka yi a watan jiya a gasar wasannin tsalle-tsalle da guje-guje ta duniya a Beijing.

Dan wasan ya ce ya yi haka ne domin ya mai da hankali wajen kare kambunsa a gasar Olympic da za a yi a Rio ta Brazil a 2016.

Rashin halartar Bolt wasannin da za a yi a Brussels zai sa Justin Gatlin ya iya dare mataki na daya a tseren mita 100 a gasar, idan har ya kammala a cikin ukun farko.