US Open: Serena za ta kara da Venus

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wannan shi ne karo na 27 da Serena da Venus za su fafata a tsakaninsu

Serena Williams za ta fafata da 'yar uwarta Venus a gasar wasan kwallon tennis ta US Open wasan daf da na kusa da karshe ranar Talata.

Serena ta doke Madison Keys ne da ci 6-3 da kuma 6-3 da ya ba ta damar kai wa wasan daf da na karshe a gasar.

Ita kuwa Venus Williams ta kai wasan zagayen gaba ne, bayan da ta casa Anett Kontaveit ta Estonia da ci 6-2 da kuma 6-1 a ranar Lahadi.

Serena Williams da Venus Williams sun kara a manyan wasannin tennis sau 26 tsakaninsu, Serena ta lashe fafatawa 15, a inda Venus ta ci wasanni 11.

Haka kuma dai a ranar Talatar Kristina Mladenovic ta Faransa za ta kece raini da Roberta Vinci ta Italiya a wasan daf da na karshe a gasar.