Nigeria ta doke Nijar da ci 2-0

Hakkin mallakar hoto the nff twitter
Image caption Wannan shi ne wasa na biyu da Sunday Oliseh ya jagoranci Super Eagles

Tawagar kwallon kafar Nigeria ta doke ta Nijar da ci 2-0 a wasan sada zumunta da suka yi a ranar Talata a Fatakwal.

Nigeria ta fara cin kwallon farko ne daga bugun fenariti ta hannun Ahmed Musa a minti na 12, sannan Moses Simon ya kara ta biyu a raga saura minti bakwai a tashi daga wasan.

Wannan shi ne wasa na biyu da sabon koci Sunday Oliseh ya jagoranci Super Eagles tun lokacin da ya maye gurbin Stephen Keshi.

Oliseh ya fara ne jagorantar Nigeria a karawar da ta yi canjaras da Tanzania a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka a ranar Asabar a Dar Es Salaam.