Gareth Bale ba zai bar Real Madrid ba

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bale ya koma Real Madrid da murza leda a shekarar 2013

Mai wakiltar Gareth Bale a harkokin tamaula ya ce dan wasan ba zai bar Real Madrid ba, duk da rade radin da ake yi zai koma Manchester United da taka leda.

Kafin a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallon kafa a karshen watan Agusta, an yi ta jita-jitar cewar Bale zai koma Old Trafford da murza leda.

Bale mai shekaru 26, ya koma Real Madrid da buga tamaula daga Tottenham a watan Satumbar 2013, a matsayin dan wasan da aka saya mafi tsada kan kudi £85m.

Da aka tambayi wakilin Bale, Jonathan Barnett kan gaskiyar labararin cewar dan wasan na son barin Madrid sai ya ce batun babu gaskiya a ciki.

Ya kuma ce ba zai ce komai ba kan batun Manchester United ta yi zawarcin Bale, illa dai ya kara da cewar da wahala dan kwallon ya koma Ingila taka leda.

Bale ya saka hannu kan yarjejeniyar shekaru shida a Real Madrid a 2013.