Roma za ta bai wa 'yan gudun hijira tallafi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hankalin duniya ya karkata ga halin da 'yan gudun hijira ke ciki

Roma ta ce za ta bai wa wani shirin taimaka wa 'yan gudun hijira kudi da zai kai sama da rabin yuro miliyan daya don amfanin sansanin da aka kafa a sassa daban-daban na duniya.

Tuni shugaban hukumar Roma, Jim Pallotta ya kafa asusun gaggawa wanda aka yi wa lakani da 'kwallon kafa ma ta damu' wanda zai samar da kudaden tallafin ga 'yan gudun hijirar.

Roma ta fara tara kudin da ya kai yuro 575,000 domin bai wa jami'an da suke kula da 'yan gudun hijira da suke fadin duniya.

A makon jiya Bayern Munich ta sanar da cewa za ta tanadi filin atisaye domin taimakawa 'yan gudun hijira da kuma kudin da zai kai £730,000 domin rage musu radadin da suke ciki.

Haka ma kwamitin Olympics na duniya ya sanar da cewa zai kafa asusun gaggawa da zai kai kudi fam miliyan daya da dubu 300 domin taimakawa 'yan gudun hijirar.