Rooney zai kafa tarihin ci wa Ingila kwallaye

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rooney da Charlton sun ci wa Ingila kwallaye 49 kowannensu

Watakila Wayne Rooney ya kafa tarihin dan wasan da yafi ci wa tawagar kwallon kafar Ingila kwallaye a ranar Talata a karawar da za su yi da Switzerland a Wembley.

Ingila wacce ke mataki na daya a rukuni na biyar, za ta fafata da Switzerland ne a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da za a yi a Faransa a 2016.

Rooney kyaftin din Ingila ya yi kan-kan-kan da Sir Bobby Charlton wajen ci wa Ingila kwallaye, kowannensu ya zura kwallaye 49 a raga.

Dan wasan wanda ya fara buga wa babbar tawagar Ingila tamaula a 2003, ya yi mata wasanni 106.

Shi ma Bobby Charlton wasanni 106 ya buga wa babbar kungiyar kwallon kafar Ingila, wacce ya yi mata wasanni tsakanin 1958 zuwa 1970.

Sauran wasannin da za a buga sun hada da:

  • Belarus v Luxembourg
  • Macedonia v Spain
  • Slovakia v Ukraine
  • Lithuania v San Marino
  • Slovenia v Estonia
  • Liechtenstein v Russia
  • Moldova v Montenegro
  • Sweden v Austria