Yarima Ali zai sake yin takarar kujerar Fifa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wannan ne karo na biyu da Yarima Ali zai yi takarar kujerar Fifa

Yarima Ali Ali Bin Al Hussein na Jordan ya sanar da aniyarsa ta sake yin takarar kujerar Fifa a karo na biyu ranar Laraba a jordan, domin maye gurbin Sepp Blatter.

Yarima Ali ya fafata a watan Mayu da Sepp Blatter wanda aka zaba karo na biyar ya jagoranci hukumar a watan Mayu.

Haka kuma shi ne mutun na uku da ya bayyana aniyarsa ta son zama shugaban Fifa bayan shugaban hukumar kwallon kafar Turai Michel Platini da kuma tsohon jami'in Fifa Chung Mong-joon.

Sepp Blatter ya amince ya sauka daga shugabantar Fifa bayan da zargin cin hanci da rashawa da ya mamaye hukumar.

Za a yi zaben wanda zai maye gurbin Sepp Blatter a ranar 26 ga watan Fabrairun 2016.