Ina addu'a a doke Real Madrid - Pique

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Pique bai da farin jini a wurin magoya bayan Real Madrid

Dan kwallon Barcelona, Gerard Pique ya ce zai ci gaba da adawa da Real Madrid duk da cewar magoya bayan kulob din na yi masa sowwa.

Dan shekaru 28, ya ce a koda yaushe yana fata a doke Real Madrid.

"Ba zan canza hammayarmu ba. Kullum addu'a nake yi a samu galaba a kan Real Madrid," in ji Pique.

A karshen mako a lokacin wasan Spain tsakaninta da Slovakia wasu 'yan Spain masu goyon bayan Real sun yi masa sowwa.