Villas-Boas zai bar kungiyar Zenit

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Koci Villas-Boas zai bar kungiyar Zenit

Andre Villas-Boas ya ce zai yi murabus daga kocin kulob din Zenit St. Petersburg a karshen kakar wasan bana, bayan da aka dakatar da shi daga yin murabus din a lokacin bazara.

Kocin dan kasar Portugal ya lashe gasar Firemiya ta Rasha da kulob din Zenit a kakar wasan bara a lokacin da yake kan ganiyarsa, amma a tsawon zamansa a kulob din St. Petersburg al'amura sun sauya inda yanzu haka aka dakatar da shi daga buga wasanni shida bayan da ya yi fada da wani jami'in wasa.

Kafofin watsa labarai na Turai sun danganta Villas-Boas da kungiyoyi da dama na kasashe daban-daban, wadanda suka hada da Real Madrid, amma ya ce shugabannin kungiyar Zenit sun hana shi yin murabus.

A wani tsokaci da ya yi a shafin intanet na Zenit, Mista Villas-Boas ya ce "Na ki amincewa da tsawaita kwantiragina, kuma a karshen kakar wasan bana zan bar kungiyar.