Sturridge ya soma horo

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Sturridge na saran zai koma kan ganiyarsa

Dan kwallon Liverpool Daniel Sturridge ya koma horo a karon farko tun bayan da aka yi masa tiyata a watan Mayu.

Sturridge mai shekaru 26, ya shafe lokaci mai tsawo yana murmurewa a Amurka.

Sai dai babu tabbas ko zai buga wasan Liverpool da Manchester United a gasar Premier ta Ingila a ranar Asabar.

A kakar wasan da ta wuce, Sturridge ya zura kwallo biyar a wasanni 18 da ya buga wa Liverpool.

Tsohon dan wasan Chelsea da Manchester City din ya shafe watanni biyar ba ya murza leda saboda rauni.