Ayew ya samu kyautar bajinta a Premier

An bai wa dan kwallon Swansea City, Andre Ayew kyautar dan wasan da yafi kowanne nuna bajinta a gasar Premier a watan Agusta.

Haka kuma an bai wa kocin Manchester City, Manuel Pellegrini irin kyautar a bangaren masu horadda 'yan kwallo.

Kyaftin din Ghana, Ayew mai shekaru 25 ya zura kwallaye uku a wasanni hudu da ya bugawa Swansea inda babu kungiyar da ta samu galaba a kan kungiyar a kakar wasa ta bana.

A na shi bangaren, Pellegrini ya jagoranci Manchester City kasancewa ta farko a kan tebur inda kungiyar ta samu galaba a wasanni hudu tare da zura kwallaye 10.