De Gea ya sabunta kwantaraginsa a United

Image caption De Gea ya haskaka a kakar wasan da ta wuce

Golan Manchester United, David De Gea ya sake sanya hannu a sabon kwataragin shekaru hudu da kulob din.

Saura kiris dan wasan dan kasar Spain, mai shekaru 24, ya koma Real Madrid a lokacin musayar 'yan kwallo, sai dai hakan bai yiwu ba saboda ba a kammala yarjejeniya a kan sa ba.

A lokacin bazara ne dai kwantaragin De Gea zai kare, amma a sabon kwantaragin yana da damar tsawaita zamansa a kulob din har shekara daya.

"Ina shaukin ganin an kammala bazara domin na ci gaba da jajircewa.Manchester United kulob ne na musamman, kuma Old Trafford ne wajen da ya cancanta na zauna domin ci gaba da haskakawa," in ji De Gea.

De Gea bai buga wa United wasan Premier ko sau saya a bana ba saboda kocin kulob din Louis van Gaal yana ganin ba zai mayar da hankali ba tun da Real na zawarcinsa.

Van Gaal ya ce ya yi matukar jin dadi kasance De Gea zai ci gaba da zama a kulob din na tsawon shekaru.