Ronaldo ya kafa tarihin cin kwallaye a Madrid

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ronaldo ya buga wa Real Madrid wasanni 204

Cristiano Ronaldo ya zama dan wasan da yafi yawan ci wa Real Madrid kwallaye a raga, bayan da ya zura biyar a karawar da suka doke Espanyol a ranar Asabar.

Madrid ta doke Espanyon da ci 6-0 a gasar La Liga wasan mako na uku da suka buga, kuma Ronaldo ne ya ci kwallaye biyar a karawar sai Karim Benzema da ya ci daya.

Hakan ne ya sa ya ci wa Madrid kwallaye 230 jumulla. Yayin da ya dara Raul wanda ke rike da tarihin wanda yafi yawan cin kwallaye a inda ya ci 228.

Haka kuma Ronaldo ya zama dan wasa na hudu da yake da tarihin yawan cin kwallaye a gasar La Liga.

Ronaldo mai shekara 30, wanda ya koma Spaniya da taka leda kan kudi £80m daga Manchester United, ya yi wa Real Madrid wasanni 204.