Everton ta doke Chelsea da ci 3-1

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Everton ta ci wasanni biyu kenan ta kuma buga canjaras a wasa biyu an doke ta sau daya

Everton ta doke Chelsea da ci 3-1 a gasar Premier wasan mako na 5 da suka kara a Goodison Park ranar Asabar.

Steven Naismith ne ya ci wa Everton kwallaye uku a raga wanda ya shiga wasan daga baya, yayin da Muhamed Besic ya ji rauni.

Chelsea ta zare kwallo daya ta hannun Nemanja Matic a inda ya buga tamaular daga yadi na 30 ta kuma fada raga.

Chelsea tana da maki hudu daga wasanni biyar da ta yi, kuma wannan shi ne kakar wasan da kungiyar ta fara da rashin kokari tun 1986.

A kakar bara wasanni uku Chelsea ta yi rashin nasara daga karawa 38 da ta yi da ya ba ta damar lashe kofin Premier.