Aguero ba zai buga karawa da Juventus ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption kwallo daya Aguero ya ci wa Manchester City a bana

Watakila dan wasan Manchester City, Sergio Aguero ba zai buga karawar da za su yi da Juventus a wasan cin kofin zakarun Turai ranar Talata ba.

Aguero ya ji rauni ne a gwiwarsa a wasan da Manchester City ta doke Crystal Palace da ci daya mai ban haushi a Selhust Park ranar Asabar.

A minti na 25 aka fitar da Aguero mai shekaru 27 daga filin wasa, bayan da Scott Dann ya yi masa keta.

A watan Disambar bara Aguero ya yi jinyar rauni wanda ya ji a gwiwarsa zuwa wata guda.

Aguero ya buga wa City wasannin Premier guda biyar, a inda ya ci kwallo daya a karawar da suka doke Chelsea ranar 16 ga watan Agusta a Ettihad.

Shi ma sabon dan wasan da City ta sayo daga Liverpool a bana Raheem Sterling watakila ba zai buga wasan da za su karbi bakuncin Juventus din ba.