"Nigeria za ta yi fice a wasan linkaya a duniya"

Image caption Yakmut ya ce Nigeria za ta fara yin shirin tunkarar wasannin Olympic na badi

Sakatare janar na hukumar wasanni na Nigeria, Alhasan Saleh Yakmut ya ce nan da shekaru hudu Nigeria za ta yi fice a wasan linkaya a duniya.

Yakmut ya ce tuni suka fara yin shirin yadda za su zakulo matasa daga yankunan karkara da makarantu wadanda suka kware a wasan linkaya, domin ba su horon da za su iya wakiltar Nigeria a wasanni.

Ya kuma ce hukumar wasanni ta Nigeria za ta inganta filayen wasanni a fadin kasar domin bai wa matasa damar rungumar wasanni daban-daban.

Haka kuma dangane da gasar wasannin Afirka da ake yi a Congo, Yakmut ya ce Nigeria za ta yi rawar gani a karshen wasannin fiye da wacce ta yi a gasar 2011.

Tawagar kwallon kafar Nigeria ta mata ta kai wasan daf da karshe a gasar wasannin Afirka duk da rashin nasara da ta yi a hannun Ivory coast da ci 2-1 a ranar Asabar.