Kungiyar PSG ta mata ta dauki Ngozi Ebere

Hakkin mallakar hoto PSG twiiter
Image caption Ebere ta wakilci Nigeria a gasar cin kofin duniya da Canada ta karbi bakunci

Kungiyar kwallon kafa ta mata ta Paris Saint-Germain ta dauki 'yar wasan Nigeria Ngozi Ebere domin ta buga mata tamaula.

Ngozi mai shekaru 24, ta rattaba hannu kan yarjejeniyar shekaru biyu da PSG ta Faransa.

'Yar wasan ta koma Paris Saint-Germain ne daga kulob din Rivers Angels na Nigeria.

Ngozi ta wakilci tawagar Nigeria a gasar kwallon kafa ta mata na cin kofin duniya da Canada ta karbi bakunci a bana.