Yanzu ake yi da ni a Real Madrid - Bale

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan ne karon farko da Real Madrid za ta fafata da Shakhtar Donetsk

Gareth Bale ya ce yanzu ne yake jin yana bayar da gagarumar gudunmawa a Real Madrid tun lokacin da ya koma Madrid da taka leda.

Bale ya sha fama da suka daga magoya bayan Madrid kan cewar baya taka rawar gani a kulob din tun lokacin da aka sayo shi £85m daga Tottenham a 2013.

Sai dai kuma dan wasan ya ci wa Madrid kwallaye uku ya kuma bayar da tamaular da aka zura kwallo a raga sau uku a kakar bana.

Real Madrid za ta kara ne da Shakhtar Donetsk a wasan gasar cin kofin zakarun Turai a ranar Talata.

Wannan shi ne karon farko da Madrid za ta fafata da Shakhtar Donetsk a kokarin ganin ta lashe kofin zakarun Turai na 11, bayan da Juventus ta fitar da ita daga gasar.