Super Eagles za ta kara da Congo da Kamaru

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nigeria na son dawo da tagomashinta a harkar kwallon kafa

Tawagar kwallon kafa ta Nigeria za ta kara da ta Congo da Kamaru a wasannin sada zumunta domin fuskantar wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya na 2018.

Super Eagles za ta fara fafatawa ne da Congo a Antwerp ranar 8 ga watan Oktoba, sannan ta yi gumurzu da Kamaru kwanaki uku tsakani a Brussels na kasar Belgium.

Oliseh na fatan wasan sada zumuntar da zai buga zai zama zakaran gwaji a karawar da zai yi da Djibouti ko kuma Swaziland a watan Nuwamba a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya.

Oliseh ya fara jan ragamar Super Eagles a karawar da suka tashi canjaras da Tanzania a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a 2017.

Haka kuma kocin ya jagoranci tawagar wasan sada zumunta da Nigeria ta doke Nijar da ci 2-0 a Fatakwal.

Nigeria ta halarci gasar cin kofin duniya da aka yi a Barazil a 2014 a inda ta kai wasan zagaye na biyu karkashin koci Stephen Keshi.