Za a yi wa Wilshere tiyata a kafarsa

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption A shekarar 2011 ne Wilshere ya ji rauni a kafarsa ta hagu da har yanzu yake fama da jinya

Likitoci za su yi wa dan wasan Arsenal, Jack Wilshere tiyata a kafarsa ta hagu, kuma ana sa ran zai yi jinyar watanni uku idan an kammala aikin.

Wilshere ya ji rauni ne a cikin watan Agusta, kuma an yi hasashen zai murmure a watan Satumba, bayan kammala buga wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai.

Sau biyu ana yi wa Wilshere aiki a kafarsa ta hagu a bara, bayan da ya ji rauni a karawar da suka yi da Manchester United a watan Nuwambar na 2014.

Wilshere na fama da jinya a kafarsa ta hagu tun lokacin da ya gamu da raunin a 2011, wanda ya yi jinyar watanni 15 a lokacin.