Ba na jure wa rashin nasara a wasanni - Mourinho

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea tana mataki na 17 a kan teburin Premier

Jose Mourinho ya ce rashin nasara a wasan kwallon kafa wani bakon abu ne a wajensa.

Mourinho ya yi wannan kalaman ne dangane da rashin nasara da Chelsea ke yi a wasannin bana, wanda rabon da ta yi hakan tun shekaru 29 da suka wuce.

Chelsea ta yi rashin nasara a hannun Everton a gasar Premier ranar Asabar, kuma shi ne karo na uku da aka doke ta a wasanni biyar da ta buga.

Wannan sakamakon ya sa Chelsea wacce ta lashe kofin Premier na bara tana mataki na 17 a kan teburin Premier da maki hudu kacal.

Mourinho ya ce "Ba na cikin farin ciki da halin da kungiyar Chelsea ta tsinci kanta, kuma ban saba da rashin nasara a wasanni na ba, amma zan karbi kaddara na saba da hakan".

Chelsea za ta karbi bakuncin Maccabi Tel Aviv a gasar cin kofin zakarun Turai a ranar Laraba.