Dinamo Zagreb ta doke Arsenal 2-1

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsenal ta karasa karawar da 'yan wasa 10 a cikin fili

Arsenal ta sha kashi a hannun Dinamo Zagreb da ci 2-1 a gasar cin kofin zakarun Turai da suka kara a ranar Laraba.

Dinamo ta fara cin kwallon farko ne a minti na 24 da fara tamaula, bayan da Oxlade-Chamberlain ya ci gida, sannan ta kara ta biyu ta hannun Junior Fernandes.

Arsenal ta zare kwallo daya ta hannun Theo Walcott saura minti 11 a tashi daga wasan.

Arsenal ta karasa wasan da 'yan kwallo 10 a fili, bayan da aka bai wa Olivier Giroud jan kati saboda ketar da ya yi wa Ivo Pinto.

A karawa ta biyu a gasar Arsenal za ta karbi bakuncin Olympiacos ta Girka a ranar Talata 29 ga watan Satumba a Emirates.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga:

  • Roma 1 - 1 Barcelona
  • Chelsea 4 - 0 Maccabi Tel Aviv
  • Bayer Levkn 4 - 1 BATE Bor
  • Olympiakos 0 - 3 Bayern Mun
  • Dynamo Kiev 2 - 2 FC Porto
  • KAA Gent 1 - 1 Lyon
  • Valencia 2 - 3 Zenit St P