Hector Moreno ya nemi afuwar Shaw

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shaw zai yi jinya mai tsawo kafin ya dawo buga wa United tamaula

Mai tsaron bayan PSV Eindhoven, Hector Moreno, ya nemi afuwa saboda ketar da ya yi wa Luke Shaw, dan wasan Manchester United.

Shaw ya karye a wuri biyu ne a kafarsa bayan da Moreno ya yi masa keta a wasan da United ta sha kaye a hannun PSV Eindhoven a Gasar cin kofin Zakarun Turai.

Shaw ya shafe mintuna 10 ana ba shi agajin gaggawa kafin ya bar cikin filin a karawar da suka yi ranar Talata a Holand.

Moreno mai shekaru 27 ya ce "Ban ji dadi ba dana zama sanadiyyar jin raunin Shaw, amma ina neman afuwa".

Hukumar kwallon kafar Turai ba ta da niyyar sake kallon ketar da aka yi a wasan ta faifan bidiyo. Kasancewar alkalin wasan bai hukunta Moreno ba, ita ma ba za ta dauki wani mataki ba.