Rashin sa'a ne ya sa Zagreb doke mu -Wenger

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Wenger dai bai saka golansa Cech da mai tsaron gida Monreal a wasan ba.

Manajan kungiyar Arsenal Arsene Wenger ya ce kungiyar ta yi rashin sa'a ne kawai a wasan da Dinamo Zagreb ta doke ta da ci 2-1 wasansu na farko na gasar zakarrun Turai

Wenger dai ya canza 'yan wasa har sau shida a yayin wasan wadda ta biyo bayan galabar da Arsenal din ta samu kan Stoke ranar Assabar.

An ba dan wasan gaba na kungiyar Olivier Giroud katin kora a minti na 40 abin da Wenger ya ce tsautsayi ne.

'' Na yi imanin cewa ci na farko an yi shi ne ta satar fage kuma matakin korar da aka dauka kan dan wasana ya yi tsauri'' in ji Wenger.

Karin bayani