Murray zai yi kyautar Fam 50 kan kowane ci

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tun a 2014 ne Murray ya shiga sahun masu ba UNICEF gudunmawa

Andy Murray ya yi alkawalin bayar da kyautar fam 50 kan kowane ci daya da ya yi ga gidauniyar UNICEF har zuwa karshen wannan kakar.

Shahararren dan wasan Tennis din ya ce zai yi hakan ne domin taimaka wa 'yan gudun hijira.

Murray mai shekaru 28 ya ce kwararar da 'yan gudun hijira ke yi domin neman mafaka a Turai, ita ce ta sa ya dauki wannan matakin.

"Saboda ganin irin hotunan da ake nunawa ta kafafen watsa labarai ne ya sa na ji cewa ya kamata in yi wani abu'' in ji shi.

Karin bayani