Za a tasa keyar jami'in FIFA zuwa Amurka

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Figueredo dai tsohon mataimakin shugaban Conmebol ne

Kasar Switzerland ta amince ta tasa keyar jami'in hukumar kwallon kafa ta (FIFA) da ake zargi da karbar rashawa zuwa Amurka.

Eugenio Figueredo dan kasar Uruguay na daga cikin jami'an hukumar su bakwai da aka kama a birnin Zurich ranar 27 ga watan Mayu.

Ana zarginsa da karbar rashawa ta miliyoyin daloli dangane da shirya gasar kasashen nahiyar kudancin Amurka ta Copa America, inji ma'aikatar shari'a ta kasar.

Mr Figueredo na da kwanakki 30 na daukaka karar amincewa da tasa keyar tasa zuwa Amurka.

Karin bayani